728x90 AdSpace

  • Latest News

    Popular Posts

    Tuesday, March 21, 2017

    Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu

    Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu
    Har yanzu tsuguni bata kare ba a game da batun gayyatar shugaban hukumar kwastan ta kasa kanar Hamid Ali, mai ritaya zuwa majalisar dattawa, domin sanata Ali Ndume ya ce yana da niyyar shigar da kara a kansa.
    Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu
    Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu
    Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa yana da niyyar shigar da karar shugaban hukumar kwastan dinne a sakamakon wata sabuwar doka da shugaban ya bullo da ita wadda ta bukaci biyan kudin futo kan dukkan motocin da ke cikin kasar komai tsufansu.
    Sanata Ndume, ya bayyana cewa wannan doka da shugaban hukumar kwastan ya bullo da ita ta sabawa alkawarin da suka yiwa al’ummar Najeriya, ta dalilin haka ne Ndume, ya ce yayi niyyar kai shugaban kotu a madadin jama’ar kasa.
    Ya kuma kara da cewa ‘yan majalisar dattawan sun kauce, domin a maimakon su yi abin da ya dami jama’a, sai suka raja’a kan maganar sa kayan sarki, kuma daya daga cikin abinda bai amince da shi ba, shine yadda wasu suka mayar da majalisar tamkar fadar wani da wani.
    Da dama daga cikin dattawan suna ganin yadda aka mayar da majalisar tamkar fadar Saraki da Dino, kuma ya kamata su dauki mataki akan wasu abubuwa da ke gudna a majalisar amma sun yi kunnen uwar shegu wai da sunan a zauna lafiya.

    Shi kuwa Sanata Kabiru Marafan Gusau, ya ce yana matukar goyon bayan da majalisa ta dauka akan shugaban hukumar kwastan din, domin idan an duba da kyau, majalisar dattawa aikinta ne.
    • Blogger Comments
    • Facebook Comments

    0 comments:

    Post a Comment

    Item Reviewed: Wata sabuwa! Sanata Ndume zai maka hukumar kwastam kotu Rating: 5 Reviewed By: Goodman Offin
    Scroll to Top